Wannan shine fassarar shaharraren littafin nan da aka fi sani da suna Huqbatun Minat Tarikh wanda ya fede biri har wutsiya a cikin ingantaccen tarihin abinda ya faru bayan wafatin Annabi (SAW) har zuwa shahadar sayyiduna Hussain (RA) a karbala.
Yana da matukar muhimmanci kowane musulmi ya karanta wannan littafi da tsarkakkiyar niyya da adalci don jin halin da sahabbai suka tsinci kansu. ALLAH YA KARA MASU YARDA