DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Wannan littafi TUNANINKA KAMANNINKA yunkuri ne mai kyau wajen kyautata dabi'un al'umma tare da dora su bisa tafarkin da zai basu daukaka a duniya da lahira. Marubucin ya nutsu wajen fahimtar halin dan Adam da kuma irin cutar dake damun zuciyarsa, sannan kuma ya bayar da maganin cututtukan. Hakika, a ganina ya gano maganin. Duk wanda ya sha maganin da Alhaji Bashir Othman Tofa ya ba wa zuciya a wannan littafi, to ya waraka! Wannan kadan kenan daga ta'alikin da Dan Masanin Kano Alhaji (Dr.) Yusuff Maitama Sule yayi wa littafin.