Wannan application ne da ke koyar da yadda ake sallah bisa koyarwar ahlubaiti (a.s) cikin harshen Hausa.
A cikinsa mun yi bayanin hukunce-hukuncen da suka shafi shekarun balaga da kuma takalidi sannan da bayanin a kan tsarki da najasa.
Harwayau akwai cikkaken bayani akan yadda ake sallah tun daga kiran sallah da ikama har zuwa sallamewa. Sannna da bayanin sallar aya da kuma muhimmancin sallar jam’i.
Muna fatar wannan application ya amfanar da miliyoyin al’ummar Musulmi masu jin harshen Hausa kuma ta zama sadakatul jariya garemu,iyayenmu da wanda suka bada gumuwa har zuwa kammalawar wannan aikin.