Babban Aboki Manhaja ce ta littafin koyar da hukunce-hukunce Shari'a ce a bisa fatawar Ayyatullah Sayyid Ali Khamne'i {Allah ya ja kwanansa}, wanda Sheikh Yusuf Umar Judi ya tsara kuma ya rubuta.
Wannan Manhajar {Application} zai taimaka wa miliyoyin mabiya ahlulbaiti {a.s} musamman masu jin harshen Hausa domin wannan Manhajar ta ƙunshi abubuwa da dama da suka shafi Ibada da hukunce-hukunce tun daga matakin tsarki zuwa yadda ake Salla da kuma wasu mas'aloli da ya ke da muhimmanci ga kowane Musulmi ya sansu.
A Kashin Farko na Wannan Manhajar an yi bayanin hukunce-hukunce kamar haka; Ruwa da kashe-kashensa,abubuwan da suke Najasa da kuma yadda ake kama ruwa da alwala da kuma cikkken bayanin yadda ake taimama.
Bugu da kari, a kashi na biyu ya tattaro bayanin muhimmancin Salla da kuma Salloli na wajibi,abubuwan da ake gabatar kafin Salla, wajiban salla da kuma abubuwan da ke bata Salla da kuma bayanin yadda za mu salla.Har ila yau, a cikin wannan Manhajar an yi bayanin mas'aloli daban-daban.
Muna fatan wannan manhajar ya amfani miliyoyin al'umma musamman masu kishin ruwan neman ilmin yadda ake Ibada bisa koyar ahlulbaiti. Mun Gode.