Wannan Manhaja, mai suna “MU SAN KWAMFUTA” an samar da itane da nufin inganta fahimtar Na’urar Kwamfuta cikin harshen Hausa a matakin farko. Wannan yunkuri muna fatan ya amfanar da dukkan mai sha’awa ko ta’ammali da na’urorin zamani domin inganta al’amuran rayuwar yau da kullum.