Umar Abdul-Aziz Baba wanda akafi sani da (Fadar Bege) An haife shi a garin Garko karamar Hukumar Wudil a da, wanda a yanzu tazama Karamar Hukuma mai zaman kanta a Jihar Kano, a ranar Alhamis a shekarar alib 1974. Shi dai Umar abdul'aziz shahararren mawakine ne, na begen Annabi Muhammadu (s.a.w) a cikin harshen Hausa. Matashine maijini ajika, allah yajikanshi ameen..
Mahaifinsa Mal Umar, mai Unguwa ne a wani kauye dake garin Garko, bayan rasuwar mahaifin Fadar Bege lokacin yana dan shekara hudu (4) sai suka dawo Karamar Hukumar Wudil da zama shida mahaifiyarsa mai suna Malama Hadiza, kasancewar dama aikine yakai mahaifin nasa Mai Unguwa garin na Garko lokaci da take hade da karamar hukumar Wudil.