Alhamdulillah! Ga COMPLETE TARJAMA da TAFSIRIN HAUSA NA ƊAHIRU BAUCHI wanda kuke sauraro a akwatunan rediyonku. Yanzu zaku iya sauke complete volume ɗin a wayoyinku domin sauraro a kowane lokaci ba tare da intanet ba
TAFSIRIN MALAM ƊAHIRU BAUCHI BAƘARA-NASI AUDIO OFFLINE
FULL QUR'AN TARJAMA ARABIC TO HAUSA LANGUAGE OFFLINE
Yabo da godia su tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki.
Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Ga ma'abota sauraron Tafsirin Alƙur'ani Mai Girma muna masu ƙaddamar muku da wannan manhaja mai muhimmanci mai ɗauke da Tafsirin alƙurani mai Girma tare da babban mashahurin malamin nan gwanin tafsirin alkurani wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi Allah Ya kiyaye shi.
A baya mun ƙaddamar muku da manhaja mai ɗauke da cikakken Tafsirin alƙur'ani mai Girma na Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam Rahimahullah kana a ƴan kwanakin nan muka kawo muku manhajar Tafsirin alƙur'ani mai Girma na babban malamin nan da ƙasar Saudia ta karrama ta kuma naɗa shi Muftin Najeriya wato shine Malam Abubakar Mahmoud Gumi Rahimahullah. Toh a yau, cikin ikon Allah muna masu kawo muku manhajar Tafsirin Littafin Allah tare da ɗaya daga cikin manyan maluman na Najeriya shine Sheikh Dahiru Usman Bauchi Allah Ya ƙara masa lafia da nisan kwana mai amfani tare da imani da kuma kyawawan ayyuka nagari Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Menene ma’anar Kalmar tarjama da ma’anar Kalmar tafsir kuma menene banbancin da ke tsakninsu?
A wajen malaman lugga: T R J M, wadannan ne bakaken da suka hada Kalmar tarjama, wato jam’in (tarjiman) shi ne wanda yake yin tarjama, yake fassara magana, ana cewa wane ya tarjama maganar wani: ma’ana ya bayyana shi ya fayyace shi, haka ma, wane ya tarjama maganar waninsa. Ma’anar ya fassara ta da wani yaren da ba nasa ba. Amma a isdilahi (wato a wajen masana tarjama), tarjama ita ce cirato magana daga wani yare zuwa wani kamar a nakalto daga farisiyya zuwa arabiyya.
A yayin da ana tsago Kalmar tafsiri daga “fassara” ko daga “safara” mafi yawan masana lugga sun tafi kan cewa ma’anar Kalmar tafsiri da aka samo ta daga fasara tana nufin ya bayyana ya yaye. Kuma masana sashen suka ce ma’anar tafsiri ita ce, gusar wa lafazi murdiya da kullin da ke cikin lafazi mai mishkila, ma’ana lafazi mai matsala wajen bada ma’anar da ake nufi. Kuma allama daba’daba’i ya yi ta’arifin sa a inda yake cewa: shi ne bayyana ma’anonin aya da yaye manufofinta da abubuwan da take nuni zuwa gare su.
Abubuwan dake cikin wannan manhaja ta Tafsirin Dahiru Bauchi da kuma fasalin yadda take aiki:
1. Cikakken* Tafsirin Littafi Mai Tsarki Na Sheikh Dahiru Usman Bauchi MP3
2. Tarjamar Alkurani mai Girma Rubutacciya daga Larabci zuwa Hausa
3. Wannan app na aiki ba tare da bukatar data ba
4. Zaku iya rubutawa da duba sunan wata surah domin zuwa ga tafsirinta cikin sauki
5. A bangaren Tarjama shima zaku iya rubuta lambar aya domin zuwa gareta cikin sauki
6. Zaku iya canja gudun karatun na audio
7. Zaku iya saita timer domin sauraron Tafsirin na wani lokaci kafin daga bisani karatun ya tsayar da kansa da kansa
Dahiru Bauchi Malami ne na addinin Musulunci a Najeriya. Babban malamin addinin Musulunci ne mai riko da tafarkin sufaye, Shehu ne kuma mukaddami ne a Dariƙar Tijjaniyya, yana Gabatar da tafsirin sa na Al'qur'ani da salon tafsirin kur’ani da kur’ani, fassara Kur'ani da Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, fassara Kur'ani da maganganun Sahabbai da Tabi'ai da magabatan Bayi na kwarai. Yana tafsiri ne a Nijeriya a garin Kaduna a Babban Masallacin Juma'a na Tudun-Wada kaduna ta kudu, Wanda dansa yake ja masa baki, amma shi mazaunin garin Bauchi ne.
Babu talla cikin wannan manhaja kuma bama karbar wani bayani daga gareku.
Idan kunji daɗin wannan manhaja, don Allah ku aiketa zuwa ga yanuwa Musulmi ta kafafenku na sadarwa.
* Muna matakin farko na gina wannan manhaja don haka za ku ga 403 files maimakon 421 amma in shaa Allahu ku saurari update. Ku sayi app ɗin tun yanzu don zamu ƙara farashin bayan update.